Publication : 16 March 2026
Update : 16 March 2026
Ya ce ƙawancen na iya fuskantar makoma mara kyau idan ƙasashen Turai ba su taimaka ba
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙungiyar tsaro ta NATO na iya fuskantar makoma “mummuna” idan ƙasashen da ke kawance da Amurka ba su taimaka wajen buɗe Mashigar Hormuz ba, wadda Iran ta rufe kuma ke da muhimmanci wajen jigilar mai a duniya.
A wata hira da jaridar Financial Times ya yi a ranar Lahadi, Trump ya ce kamar yadda Amurka ta taimaki Ukraine a yaƙin da take yi da Rasha, haka ma yake sa ran ƙasashen Turai za su taimaka wajen tabbatar da tsaron mashigar. Ya ce rufe mashigar ya haddasa tashin gwauron zabi na farashin makamashi a faɗin duniya.
Trump ya bayyana cewa ya dace ƙasashen da ke cin gajiyar mashigar su bayar da gudunmawa domin tabbatar da tsaro a yankin, inda ya ce yana bukatar jiragen ruwa na musamman domin cire nakiyoyi da kuma jami’an da za su kare yankin daga barazana.
Ya kuma bayyana cewa Amurka na tattaunawa da ƙasashe bakwai domin samar da tsaro a Mashigar Hormuz, tare da cewa har yanzu ana ci gaba da tuntuɓar Iran, amma ya nuna shakku ko ƙasar a shirye take don tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin.
A halin yanzu dai kasuwannin mai sun girgiza sakamakon rashin tabbas kan tsawon lokacin rikicin, inda farashin ɗanyen mai na West Texas Intermediate ya haura dala 100.22 kan kowace ganga, yayin da Brent ya kai dala 106.11 kan kowace ganga.
Tushen labari: Newstimehub
Central African Republic to accept third-country deportees from US, sources tell Reuters
The Central African Republic has agreed to take in migrants from other countries deported by the United States, two sources with knowledge of the matter told Reuters.
South Africa says Accra engaging in 'public spectacles' during repatriation of Ghanaian citizens
South Africa has warned Ghana it would "not tolerate public spectacles" in the evacuations of Ghanaian citizens from the country over anti-immigrant tensions.
Senegal National Assembly Speaker Sonko re-elected leader of majority party PASTEF
The speaker of Senegal's parliament, Ousmane Sonko, won re-election on Saturday as head of the majority party, PASTEF.
Most Read
All rights reserved. Newstimetr © 2023