Dollar

41,1828

0.23 %

Euro

48,1704

-0.04 %

Gram Gold

4.563,1300

1.19 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A cikin wasikar da ta aika wa Uwargidan Shugaban Amurka, Emine Erdoğan ta jaddada cewa 'yancin kowane yaro na girma cikin aminci haƙƙi ne na duniya baki ɗaya, dole ne a kare shi ba tare da la’akari da wurin zama, jinsi ko addini ba.

Matar Shugaban Turkiyya ta aika wasiƙa ga Melania Trump, ta buƙaci ta nuna goyon baya ga yaran Gaza

Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya, Emine Erdogan, ta rubuta wasiƙa zuwa ga Uwargidan Shugaban Ƙasar Amurka, Melania Trump, tana roƙonta da ta nuna irin damuwar da ta nuna wa yaran Ukraine waɗanda yaƙi ya shafa ga yaran Gaza.

A cikin wasiƙar da aka rubuta a ranar 22 ga Agustan 2025, Uwargidan Erdogan ta ambaci goyon bayan da Melania Trump ta nuna a baya, tana jaddada tausayi da ta nuna ga yara 648 'yan Ukraine da suka rasa rayukansu a rikicin.

Ta roƙi Melania da ta mayar da hankali kan wahalhalun da ake ci gaba da fuskanta a Gaza, inda aka yi kiyasin cewa mutane 62,000, ciki har da yara 18,000, sun rasa rayukansu cikin shekaru biyu da suka gabata.

‘Dole ne a kare yara’

Ta tuna ganawarsu a Fadar White House shekaru shida da suka gabata, inda Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya ta yaba da tausayi da damuwa game da bil’adama da Melania Trump ta nuna, wanda ya bayyana a cikin wasiƙarta ta baya-bayan nan zuwa ga Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin. Ta ce matsayinta na jinƙai “yana ba da fata a zukatan mutane.”

Ta kuma jaddada cewa 'yancin kowane yaro na girma cikin aminci haƙƙi ne na duniya baki ɗaya, dole ne a kare shi ba tare da la’akari da wurin zama, jinsi ko addini ba

“Kalaman ‘ƙananan yaran da ba a san su ba’ da aka rubuta a kan likkafanin dubban yara na Gaza da ba a iya gano sunayensu suna haifar da raunuka masu tsanani a kan lamirinmu na bai ɗaya,” in ji ta a cikin wasiƙarta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#