Matakin ya jawo suka daga Turkiyya, Masar, Qatar da Jordan

Isra’ila Ta Amince Da Rijistar Filaye A Gabar Yamma

Gwamnatin Isra'ila ta amince da wani tsari na yin rijistar filaye a Gabar Yamma da aka mamaye, matakin da ya jawo suka daga ƙasashe da dama da kuma masu fafutukar kare haƙƙin Falasdinawa, waɗanda suka bayyana shi a matsayin “babban kwacen filaye” da zai hanzarta mamayar yankunan Falasdinawa.
TRT Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce matakin zai ba da damar fayyace haƙƙoƙi da warware takaddamar shari’a kan filaye, tana mai cewa an buƙaci hakan ne sakamakon yin rijistar filaye ba bisa ƙa’ida ba a yankunan da Hukumar Falasdinawa ke iko da su.
TRT Hausa

Sai dai Turkiyya, Masar, Qatar da Jordan sun soki matakin, suna masu cewa ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa. Ankara ta ce matakin yana nufin tilasta ikon Isra’ila kan Gabar Yamma da faɗaɗa ayyukan matsugunan ‘yan kama wuri zauna.
TRT Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayyana cewa wannan tsari yana ƙara tauye haƙƙin Falasdinawa tare da lalata duk wani yunƙuri na samar da zaman lafiya da mafitar ƙasashe biyu, tana mai jaddada cewa Isra’ila ba ta da ikon mallakar yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
TRT Hausa

Gwamnatin Masar ta kira matakin da hatsari mai nufin ƙarfafa ikon Isra’ila kan yankunan Falasdinawa, yayin da Qatar ta yi Allah wadai da shirin mayar da filayen Gabar Yamma zuwa abin da ta kira “kadarorin ƙasa,” tana mai cewa hakan zai hana Falasdinawa ‘yancinsu.
TRT Hausa

Hukumar Falasdinawa ta yi kira ga shiga tsakani na ƙasa da ƙasa domin hana fara wani sabon tsarin mamaya da ke barazana ga kafuwar ƙasar Falasdinu a nan gaba.
TRT Hausa

Ƙungiyar Isra’ila mai adawa da mamayar yankunan Falasdinawa, Peace Now, ta bayyana matakin a matsayin “babban kwace filaye,” tana mai cewa zai canza tsarin mallakar ƙasa a yankin gaba ɗaya.
TRT Hausa

Rahotanni sun ce za a sake buɗe rajistar filaye a Gabar Yamma a karon farko tun 1967, kuma tsarin zai shafi Yankin C ne kawai, wanda ke ƙarƙashin ikon tsaro da gudanarwar Isra’ila kuma ya ƙunshi kusan kashi 60 cikin 100 na yankin.
TRT Hausa

A halin yanzu, sama da ‘yan Isra’ila 500,000 na zaune a matsugunai da wurare a Gabar Yamma da aka mamaye, yayin da kimanin Falasdinawa miliyan uku ke rayuwa a yankin, lamarin da ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a duniya.
TRT Hausa

 
 
 
 
 
#