An haifi Maria Branyas Morera a San Francisco a cikin 1907 a cikin zuri'ar Catalan.

Maria Morera: Wacce ta fi kowa tsufa a duniya tana murnar cikarta shekara 117

Maria Branyas Morera, matar da ta fi tsufa a duniya, ta yi bikin cika shekaru 117 da haihuwa a yankin Catalonia na kasar Spain.

“Tsufa wani nau'in ibada ne. "Ka rasa jin ka, amma a lokacin ne ma kake ji sosai saboda kuna jin yadda rayuwa ke kasancewara, ba hayaniya ba… Sanin cewa za ka mutu na sa ka sake gane muhimmancin rayuwa," ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, tana ambato wata magana da babban malamin ɗariƙar Katolika Pedro Casaldaliga. .

Kundin bajinta na Guinness Book of World Records ya ayyana ta a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya a watan Janairun 2023, bayan da ɗaya matar da ta fi kowa tsufa ƴar Faransa Lucile Randon ta mutu tana da shekara 118.

An haife ta a San Francisco a cikin 1907 a zuri'ar Catalan, ta koma zama tare da danginta a Spain lokacin tana da shekaru takwas. A lokacin tafiyar ta Atlantika, ta zama kurma a kunne ɗaya kuma mahaifinta ya mutu saboda tarin fuka.

#