Tauraron ɗan Adam ɗin samfurin FRG-100D4, da aka harba a wani ɓangare na aikin tafiya sama da SpaceX ya yi wa laƙabi da suna Bandwagon-5 mission, na da kayayyaki da aka samar daga cikin gida da kuma wata komfuta mai aiki da AI don tafiya mai zurfi.
Kamfanin fasahar sararin samaniya na Turkiyya Fergani ya yi nasarar tura tauraron ɗan’adam ɗinsa na gwaji na shida zuwa sararin samaniya a wani ɓangare na aikin tafiya sararin samaniya na kamfanin SpaceX da aka yi wa laƙabi da suna Bandwagon-5 mission, kamar yadda kamfanin ƙere-ƙere na Baykar ya bayyana.
An tura tauraron ɗan’adam ɗin na FRG-100D4 ne daga Florida kuma ya rabu da rokar harba shi kimanin minti 63 bayan an harba ta, inda ya kai kewayen sararin samaniyar da aka tura shi na nisan kilomita 590 da misalin ƙarfe 3.07 na yamma a agogon Turkiyya (ƙarfe 12:07 a agogon GMT).
Shugaban kamfanin Baykar kuma jigo a harkar fasaha Selcuk Bayraktar ne ya kafa kamfanin fasahar sararin samaniya na Fergani kuma ya haɗa tauraron ɗan’adam ɗin ta hanyar amfani da ƙwarewa ta injiya na cikin gida.
Kamfanin ya ce FRG-100D4 na da wasu ingantattun fasahohi da taurarin ɗan’adam da suka gabace shi ba su da su.
Kayayyakinsa da aka haɗa a cikin gida sun haɗa da wasu ɓangarori na mayar da martani da sandar maganeɗisu mai juyi da mita ta maganeto da ɓangaren gwada nauyi da na’urar karɓar bayanan GPS da farantin sola mai juyi da tarin batura da modem mai sabunta kansa da eriya.
Kazalika tauraron ɗan’adam ɗin na ɗauke da wata komfuta mai aiki da ƙirƙirarriyar basira (AI) da aka haɗa domin taimaka wa tafiye-tafiye da suka fi wannan nisa.
