Wannan shafin yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Za a saki 'yan Isra'ila 14 da Falasdinawa 42 a rana ta biyu ta yarjejeniyar musayar fursunoni

Hukumomi a Isra'ila sun ce za a saki fursunonin yaki 14 'yan Isra'ila da ake rike da su a Gaza da kuma Falasdinawa 42 da ke Isra'ila bayan harin da Hamas ta kaddamar a ranar 7 ga watan Oktoba.

Za a saki fursunonin ne a rana ta biyu ta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni tsakanin Hamas da Isra'ila.

Hukumomin Fursuna sun tabbatar da cewa Falasdinawa 42 - duka maza da mata - za a sake su karkashin yarjejeniyar da aka yi wadda ta amince da yin musanyar Falasdinawa uku da dan Isra'ila daya, kuma wata majiyar gwamnatin Isra'ila ta ce za a mika mutanen 14 da aka yi garkuwa da su.

#