Isra'ila ta kwashe kwana 279 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,295 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata mutum sama da 88,241, kana mutum fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai.
0441 GMT — Cibiyar bayar da bayanai kan hakkokin ɗan'adam ta Yankunan da Isra'ila ta mamaye, B’Tselem, ta bayyana umarnin da sojojin Isra'ila suka bai wa dukkan Falasɗinawa na ficewa daga Birnin Gaza a matsayin “hauka zalla.”
A wani saƙo da ta wallafa a soshiyal midiya, cibiyar ta yi kira ga ƙasashen duniya su tsoma baki sannan su "nemi Isra'ila ta daina yaƙi nan-take”.
“Bisa ayyukan da Isra'ila take yi, da alama tana da niyyar ci gaba da yaƙi babu ƙaƙƙautawa, inda take lalata gine-gine da kashe mutane ba tare da sanin lokacin da za ta daina ba," in ji saƙon da ƙungiyar ta fitar.