Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 194 tana kai wa Falasɗinawa da ke Gaza sun kashe aƙalla mutum 33,843 da jikkata sama da mutum 76,575 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan.
0000 GMT —Rashin hankalin da Isra'ila take yi na kai wa fararen-hulan Gaza hari ya nuna gazawar sojojinta — Hamas
Ƙungiyar Hamas ta ce "haukan da masu ra'ayin Yahudanci" suke yi na kai hari a kan Falasɗinawa fararen-hula a Gaza na nuna gazawar rundunar sojin Isra'ila a yayin da ake yi mata turjiya.
"Haukan da masu ra'ayin Yahudanci suke yi a kan fararen-hula alamomi ne na gazawar sojojin mamaya kwata-kwata a yayin da suke fuskantar turjiya,'' in ji shugaban Hamas Izzat al Rishq a sanarwar da ya watsa a shafin Telegram.
Ya ƙara da cewa "Hotunan da aka ɗauka a Asibitin Shifa da ke Birnin Gaza sun nuna sojojin mamaya na ƴan Nazi suna yin kisan ƙare-dangi mafi muni a duniya a ɓangaren kiwon lafiya.''
Ya ƙara da cewa, “Goyon bayan da Amurka da ƙasashen Yamma suke bai wa haukan da masu ra'ayin Yahudanci suke yi bai sauya ba wajen faɗaɗa rikici a wannan yankin."
2100 GMT —Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 28, cikinsu har da ƙananan yara da dama, a sabbin hare-hare da ta kai wurare daban-daban a yankin Gaza da ta mamaye, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World da kafafen watsa labaran yankin.
Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mutum takwas a yankin Tuffah bayan sun kai hari kan wata motar ƴan sanda. Kazalika luguden wutar da Isra'ila ta yi a sansanin al-Maghazi da ke yankin Deir al-Balah na Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 13.
Haka kuma Isra'ila ta kashe Falasɗinawa bakwai a harin da ta kai wa wasu iyalai a sansanin Yabna da ke birnin Rafah. Ta jikkata mutane da dama a harin.