Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 3 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Marasa lafiya sun soma mutuwa yayin da asibiti daya tilo na cutar kansa a Gaza ya daina aiki

0034 GMT — Marasa lafiya sun soma mutuwa yayin da asibiti daya tilo na cutar kansa a Gaza ya daina aiki

Marasa lafiya hudu sun mutu bayan asibitin Turkish-Palestinian Friendship, wanda shi ne daya tilo da ke kula da masu dauke da cutar kansa a Gaza, ya daina aiki.

"Mutum hudu da ke fama da cutar daji sun mutu yau bayan Asibitin Turkish-Palestinian Friendship ya daina aiki saboda rashin fetur," a cewar daraktan asibitin, Subhi Skaik, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu Agency.

Ya kara da cewa: "Mutanen sun mutu ne sakamakon rashin isassun kayan aiki na asibiti."

A cewarsa, an dauke dukkan masu fama da cutar kansa daga asibitin zuwa Asibitin Dar al Salam da ke Khan Yunis a kudancin Gaza.

#