Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
0852 GMT — Kasashen duniya sun soma janye jakadunsu daga Isra'ila
Kasar Bolivia a ranar Talata ta ce ta yanke huldar dilfomasiyya tsakaninta da Isra’ila sakamakon irin harin da take kai wa Gaza.
Haka kuma kasashen Colombia da Chile su ma sun yi wa jakadunsu kiranye domin tuntuba.
Duka kasashen sun nemi a tsagaita a yakin da ake yi inda kasashen Mexico da Brazil da ke yankin Latin America su ma suka yi kira kan tsagaita wutar.
