Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI-TSAYE: Jarirai 39 na fuskantar barazanar mutuwa bayan asibiti mafi girma a Gaza Al-Shifa ya daina aiki

1020 GMT — Isra'ila ta daure malamin makaranta kan zargin sojojin kasar da aikata 'fyade'

Isra’ila a ranar Asabar ta dakatar da kuma tsare wani malamin makaranta kan sukar dakarun Isra’ila kan harin da suke kai wa farar hula da cin zarafin matan Falasdinawa inda malamin ya kira su da “masu kisan yara.”

“An tsare tare da dakatar da wani malamin makaranta daga aikinsa kan zargin sojojin Isra’ila da yi wa matan Falasdinawa fyade da kuma halasta harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba,” in ji wata sanarwa da sojin Isra’ila suka fitar.

A sakon da malamin tarihin ya wallafa a shafukan sada zumunta, ya ce tun shekarar 1948 sojojin Isra’ila ke yi wa mata fyade, sai dai ba a rubuta hakan a littattafai.

0850 — Asibiti mafi girma a Gaza Al-Shifa ya daina aiki

Jarirai akalla 39 na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon karancin iskar oksijin a yayin da Asibitin Al-Shifa mafi girma a Gaza ya daina aiki ranar Asabar sakamakon luguden wuta da Isra'ila ke yi masa ta kowanne bangare, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu.

Kazalika Ministan Lafiya na Falasdinu ya ce asibiti 20 cikin 35 sun daina aiki sakamakon bama-baman da Isra'ila ke harba musu.

0820 — Za a binne gawawwakin mutum 100 a kabari daya a harabar Asibitin Al-Shifa da ke Gaza

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu ta ce za a haka babban kabari a cikin harabar Asibitin Al-Shifa ranar Asabar sannan a binne gawawwakin mutum 100 da ke yashe a asibitin.

Da yake tattaunawa da gidan talbijin na Al Jazeera da safiyar Asabar, Darakta Janar na Ma'aikatar Dr. Munir Al-Borsh ya ce Isra'ila ta kwashe dare na uku a jere tana luguden wuta a kusa da asibitin.

“Ana yin ruwan bama-bamai kusan kowane minti daya, da nufin samun hanyar shiga asibitin,” in ji shi, inda ya kara da cewa hare-haren Isra'ila sun hana motocin daukar marasa lafiya samun damar shiga ko fita daga asibitin.

“An yi mana kawanya a harabar Asibitin Al-Shifa,” a cewarsa.

A nata bangaren, kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders (MSF) ta wallafa sako a shafin X cewa: "A sa'o'i kadan da suka gabata, ana ta kai hari babu kakkautawa a Asibitin Al-Shifa."

Ana ci gaba da gumurzu a kusa da asibotocin Gaza masu cike da jama'a, inda jami'an Falasdinu suka ce Isra'ila tana jefa musu abubuwan fashewa da yin luguden wuta. . / Hoto: AA

0750 — Lokacin surutu ya kare, ya kamata a dauki mataki kan rikicin Gaza - Raisi

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ranar Asabar ya ce lokacin surutu ya kare don haka yanzu lokacin daukar mataki ne a kan rikicin Gaza a yayin da yake kan hanyar tafiya Sudiyya domin halartar taron Kasashen Larabawa da na Musulmai.

"Batun Gaza ba na yin surutu ba. Ya kamata a dauki mataki," in ji Raisi a filin jirgin saman Tehran kafi ya tashi zuwa birnin Riyadh na Saudiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Ya kara da cewa: "A yau, hadin kan kasashen Musulmai yana da matukar muhimmanci."

Shugaba Ebrahim Raisi ya ce hadin kan kasashen Musulmai yana da matukar muhimmanci./Hoto:Reuters

0700 — Isra'ila tana harba bama-bamai da kashe 'jarirai da mata da tsofaffi' a Gaza — Shugaban Faransa Macron

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga Isra'ila ta daina harba bama-bamai kan fararen-hula a Gaza, yana mai cewa babu wata hujja ta yin haka.

A hira da BBC, Macron ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta bayan harin da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba, sai dai ya kara da cewa: "Ana harba bama-bamai da kashe wadannan jarirai da mata da tsofaffi. Babu wata hujja ta yin haka. Saboda haka muna kira ga Isra'ila ta daina."

Tsarin kiwon lafiya na Gaza "ya durkushe" amma duk da haka ana tura magunguna na musamman," a cewar jami'in WHO. / Hoto: AA

0629 GMT — An zargi Isra'ila da 'kaddamar da yaki' a asibitocin Gaza masu cike da jama'a

Ana ci gaba da gumurzu a kusa da asibotocin Gaza masu cike da jama'a, inda jami'an Falasdinu suka ce Isra'ila tana jefa musu abubuwan fashewa da yin luguden wuta.

"Yanzu haka Isra'ila ta kaddamar da yaki a asibitocin Gaza," a cewar Mohammad Abu Selmeyah, daraktan Asibitin Al Shifa.

Daga bisani ya ce Isra'ila ta kashe mutum akalla 25 a makarantar Al-Buraq da ke Birnin Gaza, inda mutanen da ta rusa wa gidaje suke samun mafaka.

Jami'ai a Gaza sun ce Isra'ila ta harba rokoki a harabar Asibitin Al Shifa, wanda shi ne mafi girma a yankin, da safiyar Juma'a, sannan ta lalata Asibitin Indonesia kuma an cinna wuta a cibiyar kula da masu ciwon kansa ta Asibitin Nasser Rantissi.

#