Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 69 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,608, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 50,594 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine

KAI-TSAYE: Jakadiyar Isra'ila a Birtaniya ta ki amincewa da samar da kasashe biyu a matsayin mafita ga yakin Gaza

0148 GMT — Jakadiyar Isra'ila a Birtaniya ta ki amincewa da samar da kasashe biyu a matsayin mafita ga yakin Gaza

Jakadainr Isra'ila a Birtaniya ta yi watsi da yiwuwar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin hanyar warware rikicin da ya biyo bayan mamayar da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasdinawa na tsawon shekaru, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Sky News.

"Ina ganin lokaci ya yi da duniya za ta fahimci tsarin Oslo ya gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma muna bukatar sake gina wani sabon tsari," in ji Tzipi Hotovely, yayin da take magana kan ranar da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kaddamar da wani harin ba-zata kan Isra'ila.

Ta kara da cewa "Isra'ila ta sani a yau kuma ya kamata duniya ta sani cewa dalilin da yasa yarjejeniyar Oslo ta gaza saboda Falasdinawa ba su taɓa son samun ƙasa kusa da Isra'ila ba, suna son samun ƙasa tun daga kogi har zuwa teku."

Hotovely ta tambayi ɗan jaridar Mark Austin, dalilin da ya sa ya damu da batun tsarin samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, bayan da ya tambaye ta ko wannan yunƙurin ya mutu ne.

Da aka tambayi ra'ayinta game da kalaman shugaban Amurka Joe Biden na cewa Isra'ila tana "rasa goyon baya" kan harin bama-bamai da take kaiwa Gaza, sai ta ce "Amurkawa suna yakar ISIS [Daesh] a Mosul, [Iraƙi], akwai mutanen da aka kashe a Mosul daidai ko fiye da na Gaza."

Hotovely ta yi iƙirarin ƙarya cewa Isra'ila "tana yin duk abin da zai hana asarar rayuka" kuma ta ce makarantun Majalisar Dinkin Duniya a Gaza "sun zama makarantun ta'addanci."

0420 GMT — Masar za ta kara yawan fetur din da ake shigawar Gaza a kullum a daidai lokacin da ake ci gaba da ayyukan jinƙai

Masar ta sanar a jiya Laraba cewa, za ta kara yawan man da ake aika wa a kullum zuwa Zirin Gaza daga lita 129,000 zuwa lita 189,000 bisa yarjejeniya da Isra'ila.

Shugaban hukumar yada labaran kasar Masar Diaa Rashwan ya bayyana cewa, kasar Masar na ci gaba da kokarin tabbatar da shigar da kayayyakin jinƙai zuwa Zirin Gaza.

Ya ƙara da cewa, tun a ranar Talatar da ta gabata ne, motocin agaji suka fara tsallakawa ta iyakar Rafah zuwa mashigar Karem Abu Salem domin aiwatar da yarjejeniya da ɓangaren Isra'ila.

Ana sa ran hakan zai saukaka isar manyan motocin dakon kaya zuwa Zirin Gaza, tare da ƙara adadinsu zuwa 60 zuwa 80 a kullum.

Rashwan ya lura cewa adadin manyan motocin da suka tsallaka daga kan iyakar Rafah zuwa Zirin Gaza ya kai 4,057 tun lokacin da aka fara shigar da kayan agaji cikin yankin daga bangaren Masar na mashigar.

#