Hare-haren da Isra'ila ta kwashe 69 tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 18,608, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 50,594 sun jikkata kana dubban na binne a karkashin baraguzan gine-gine
1205 GMT — Isra'ila ta yi shiru kan rahoton shigar da ruwan teku a cikin ramukan ƙarƙashin ƙasa na Gaza
Sojojin Isra'ila sun ci gaba da yin shiru dangane da rahotannin baya-bayan nan da ke cewa sun fara tura ruwan teku a cikin wani ramin ƙarƙashin ƙasa a Gaza da ake zargin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ce ke amfani da shi.
Tun da farko, jaridar Wall Street Journal, ta naƙalto jami'an Amurka da suka yi karin haske game da mamayar sojojin Isra'ila, ta ce matakin da aka dauka na mamaye ramukan da ruwa daga Tekun Bahar Rum na daga cikin dabarun da Isra'ila ke amfani da su wajen lalata ramukan.
A wani taron manema labarai da aka yi ta wayar tarho, wani babban jami'in sojan Isra'ila ya amsa tambayoyi kan rahoton.
Da yake nuni da gazawar bayyana takamaiman aiki, jami'in ya jaddada yunƙurin da sojojin Isra'ila suka daɗe suna yi wajen haɓaka zaɓen dabarun da suka shafi ramukan ƙrƙashin ƙasa.
Ya lura cewa akwai hanyoyi da yawa don kawar da ramukan.
Da aka tambaye shi ko sojojin Isra'ila sun fara ambaliya ko kuma suna shirin cika duk wata hanyar ƙarƙashin ƙasa, sai ya sake nanata kalaman na baya-bayan nan da babban hafsan sojin Isra'ila Herzi Halevi ya yi amma ya ki bayar da cikakken bayani.
Tun da farko, Halevi ya kira yi wa ramukan ambaliya da "kyakkyawan tunani." Isra'ilawan da Hamas ta sako a Gaza sun ce an tsare su ne a mashigin hanyar ƙarƙashin ƙasa.
Masana sun yi gargadin cewa ambaliyar ramukan yankin da ruwan teku na iya haifar da ɓarnar muhalli da ba za a iya jurewa ba.
1125 GMT — Isra'ila za ta tattauna jadawalin yakin Gaza da babban mai bai wa shugaban Amurka shawara kan tsaro
Jami’an Isra’ila za su tattauna kan jadawalin yaƙin da ake ci gaba da yi a Zirin Gaza tare da babban mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana a ranar Alhamis.
Sullivan ya isa Isra'ila a ranar Alhamis don ziyarar kwana biyu inda zai gana da Firaminista Benjamin Netanyahu da shugaban ƙasa Isaac Herzog da manyan jami'an ƙasar don tattauna batun yaƙin Gaza.
Kafar watsa labaran Isra'ila ta Channel 12 ta ce Isra'ila na shirin kawo ƙarshen wannan zagon na haren-haren da take kai wa a ƙarshen watan Janairu a bisa tsarin jadawalinta.
Washington na son kawo ƙarshen yaƙin a farkon Janairu, amma Isra'ila tana ganin hakan ba zai yiwu ba, a cewar kafar.
"Isra'ila ta ce tana buƙatar ƙarin ƴan makonni bayan kawo ƙarshen yaƙin don kammala janye dakarunta daga cikin yankin Zirin Gaza da kuma tura sy fagen kare ƙasar, sai kuma wasu da za ta bari a ciki da wajen zirin," a cewar Channel 12.
"Mataki na gaba, wanda ake sa ran zai fi tsawo, shi ne na kammala shirin akwar da Hamas," ta ƙara da cewa.
Isra'ila ta yi ƙiyasin cewa za a shafe illahirin shekarar 2024 don lalata duk wani ƙarfin sojin Hamas.
"Abu mafi muhimmanci shi ne cewa Isra'ila na son samun iko da tsaron Gaza a nan gaba," in ji kafar.
"Wannan jadawalin ya yi kama da wannan Amurka da Isra'ilan duk za su iya amincewa da shi. Ƙari a kan haka shi ne, Amurkawa na ganin babban muhimmancin batun jinƙai ga al'ummar Gaza," ta ce.
0452 GMT — Jirgin yakin Isra'ila ya kai mummunan hari a gidaje a Gaza, ya kashe gomman Falasdinawa
Jirgin yakin Isra'ila ya kai mummunan hari a Gaza da sanyin safiya, inda a kashe Falasdinawa akalla 27 tare da lalata gine-gine a birnin Rafah.
Majiyoyi da ke yankin sun rawaito cewa Isra'ila ta kai hare-hare a arewaci da kudancin Gaza, inda ta kashe mutane da dama a Khan Younis.
An kai hari a gidajen iyalan Ashour da Abu Dabaa — inda aka kashe Falasdinawa akalla 27.
Isra'ila ta kara kaimi wurin kai hare-hare a yankunan Al Daraj da Al Tuffah da ke Birnin Gaza, da kuma birnin Jabalia da ke arewaci.
0148 GMT — Jakadiyar Isra'ila a Birtaniya ta ki amincewa da samar da kasashe biyu a matsayin mafita ga yakin Gaza
Jakadiyar Isra'ila a Birtaniya ta yi watsi da yiwuwar samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu a matsayin hanyar warware rikicin da ya biyo bayan mamayar da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasdinawa na tsawon shekaru, a wata hira da ta yi da gidan talabijin na Sky News.
"Ina ganin lokaci ya yi da duniya za ta fahimci tsarin Oslo ya gaza a ranar 7 ga watan Oktoba, kuma muna bukatar sake gina wani sabon tsari," in ji Tzipi Hotovely, yayin da take magana kan ranar da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta kaddamar da wani harin ba-zata a Isra'ila.
Ta kara da cewa "Isra'ila ta sani a yau kuma ya kamata duniya ta sani cewa yarjejeniyar Oslo ta gaza saboda Falasdinawa ba su taɓa son samun ƙasa kusa da Isra'ila ba, suna son samun ƙasa tun daga kogi har zuwa teku."
Hotovely ta tambayi ɗan jaridar Mark Austin, dalilin da ya sa ya damu da batun tsarin samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, bayan da ya tambaye ta ko wannan yunƙurin ya mutu ne.
Da aka tambayi ra'ayinta game da kalaman shugaban Amurka Joe Biden na cewa Isra'ila tana "rasa goyon baya" kan harin bama-bamai da take kaiwa Gaza, sai ta ce "Amurkawa suna yakar ISIS [Daesh] a Mosul, [Iraƙi], akwai mutanen da aka kashe a Mosul daidai ko fiye da na Gaza."
Hotovely ta yi iƙirarin ƙarya cewa Isra'ila "tana yin duk abin da zai hana asarar rayuka" kuma ta ce makarantun Majalisar Dinkin Duniya a Gaza "sun zama makarantun ta'addanci."
0420 GMT — Masar za ta kara yawan fetur din da ake shigarwa Gaza a kullum
Masar ta sanar a jiya Laraba cewa, za ta kara yawan man da ake aika wa a kullum zuwa Zirin Gaza daga lita 129,000 zuwa lita 189,000 bisa yarjejeniya da Isra'ila.
Shugaban hukumar yada labaran kasar Masar Diaa Rashwan ya bayyana cewa Masar na ci gaba da kokarin tabbatar da shigar da kayayyakin jinƙai zuwa Zirin Gaza.
Ya ƙara da cewa, tun a ranar Talatar da ta gabata ne, motocin agaji suka fara tsallakawa ta iyakar Rafah zuwa mashigar Karem Abu Salem domin aiwatar da yarjejeniya da ɓangaren Isra'ila.
Ana sa ran hakan zai saukaka isar manyan motocin dakon kaya zuwa Zirin Gaza, tare da ƙara adadinsu zuwa 60 zuwa 80 a kullum.
Rashwan ya lura cewa adadin manyan motocin da suka tsallaka daga kan iyakar Rafah zuwa Zirin Gaza ya kai 4,057 tun lokacin da aka fara shigar da kayan agaji cikin yankin daga bangaren Masar na mashigar.
0400 GMT — Harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai ya kashe Falasdinawa uku a Jenin
Wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai ya kashe Falasdinawa akalla uku a ranar Laraba a garin Jenin da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan.
Kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya rawaito cewa harin da aka kai a gabashin birnin, ya kuma jikkata mutum 10.
Tawagar kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu tana aikin mika wadanda suka jikkata zuwa asibitoci.
Sojojin Isra'ila sun kuma kai hari kan gidaje da ke unguwar ta hanyar amfani da makami mai linzami na Ener ga, lamarin da ya janyo ɓarna sosai.
Sojojin Isra'ila sun kuma kai farmaki kan wasu gidaje da ke unguwar, inda suka yi ɓarna tare da haifar da ƙazamin fada.
Da farko dai sojojin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama kan wasu gidaje uku a Jenin, inda suka kashe Falasdinawa takwas.
Ana zaman ɗarɗar a Gabar Yammacin Kogin Jordan a daidai lokacin da sojojin Isra'ila suka kai farmaki a Zirin Gaza bayan harin ba-zatan da irin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Kimanin Falasdinawa 283 aka kashe a Gabar Yammacin Kogin Jordan sakamakon hare-haren Isra'ila, yayin da wasu fiye da 4,000 ke tsare tun daga lokacin, a cewar alkaluman Falasdinawa.