Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza - ya kwana na 74 - inda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 19,453, da jikkata wasu fiye da 52,286, yayin da ake fargabar dubban mutane sun mutu a karkashin baraguzan gine-ginen da aka kai wa hari.

KAI-TSAYE: Isra’ila ta mayar da wani asibiti barikin soji a Gaza

0915 GMT — Isra’ila ta mayar da wani asibiti barikin soji a Gaza

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun mayar da asibitin Al-Awda barikin sojoji.

Ma’aikatar ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce a halin yanzu sojojin na Isra’ila na rike da Falasdinawa 240 a cikin asibitin wadanda suka hada da marasa lafiya da ma’aikatan asibitin da wadanda suka rasa muhallansu.

0811 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 25 a birnin Rafah

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 25 a birnin Rafah da ke kudancin Zirin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya bayyana.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare a cikin gidaje da asibitoci a Gaza.

Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe mutum 19,453 a Zirin Gaza wadanda akasarinsu yara ne da mata.

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ba kakkautawa a Gaza. / Hoto: Reuters

2243 GMT — Isra'ila ta kashe yarinyar da aka kashe iyaye da 'yan'uwanta a wani hari na baya

Isra'ila ta kashe wata yarinya da ta rasa ƙafa aka kuma hallaka iyayenta da 'yan'uwanta a wani harin sama da ƙasar ta kai a baya, kamar yadda mahukunta a Gaza da aka yi wa ƙawanya suka ce.

Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa a cikin daren jiya ne aka yi ruwan bama-bamai a cibiyar kula da lafiya ta Nasser da ke birnin Khan Younis a kudancin Gaza da Isra'ila ta yi wa ƙawanya, lamarin da ya yi sanadin kashe Donia Abu Mohsen mai shekaru 13 da haihuwa.

Ma’aikatar ta ce a cikin wata ‘yar gajeriyar sanarwa ta kafar sadarwa ta Telegram cewa matashiyar “ta yi shahada kuma ta bi sahun ‘yan'uwanta baki daya bayan da aka kai hari a sashen 'yan haihuwa na Asibitin Nasser,” in ji shi.

A cewar ma'aikatar, ta rasa iyayenta da dukkan 'yan'uwanta a yaƙin, kuma ta kasance ita kadai bayan ta rasa ƙafarta a wani harin da Isra'ila ta kai a baya.

Babban Daraktan Asibitin Nasser, Mohammed Zaqout, ya bayyana wannan harin da aka kai wa asibitin a matsayin "yunƙurin da Isra'ila ta yi da gangan na wargaza kowane fanni na rayuwa a Gaza."

Tun da farko, kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya yi hira da Donia a asibitin Nasser.

“Muna barci a gida sai suka jefa bama-bamai a gidanmu, kuma ba mu ji harin farko ba, mun tashi ne muka ga wuta na ci, mun tsorata, ba mu san ta yadda za mu tsere ba. Daga nan sai suka sake kawo hari na biyu da makami mai linzami, sai kuma wani ya sake biyo baya."

"Lokacin da na farka, na tarar da komai a ruguje - sai duwatsu da jini da ƙura da wuta, duk da ɓarnar da aka yi, ban ji tsoro ba, mahaifina da 'yar'uwata suna tare da ni. Mutane sun kawo ni asibiti bayan sun ceto ni yayin da suka cece ni a lokacin barci nake yi, wasu sun zo yi min tiyata, an yanke min ƙafa,” ta ƙara da cewa.

"Mahaifiyata da mahaifina da ƙanina Mohammed da ƙanwata Dalia sun yi shahada, ina fatan tafiya in sami wata ƙafa ta roba domin in yi tafiya kamar kowa."

0126 GMT — Blinken ya yi tur da harin kungiyar Houthi a wayar da ya yi da takwaransa na Saudiyya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan inda ya yi Allah wadai da hare-haren da kungiyar Houthi ta Yaman ta kai kan jiragen ruwa na kasuwanci a tekun ƙasa da ƙasa na Bahar Maliya.

"Sakataren ya kuma yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren da 'yan Houthi ke kaiwa kan jiragen ruwa na kasuwanci da ke aiki a cikin tekun ƙasa da ƙasa a kudancin Bahar Maliya, ya kuma bukaci hadin kai tsakanin dukkan abokan hulda domin tabbatar da tsaron teku," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka bayan kiran wayar.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya yi Allah wadai da hare-haren da kungiyar Houthi ke kai wa Bahar Maliya.

'Yan tawayen Houthi sun kutsa kai cikin yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ta hanyar kai hare-hare kan jiragen ruwa a muhimman hanyoyin jiragen ruwa har ma da harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan Isra'ila mai tazarar sama da kilomita 1,600 daga inda ƙungiyar take a Sanaa babban birnin kasar Yemen.

Kungiyar Houthi ta ce ta kaddamar da wani harin jirgin sama mara matuƙi kan wasu jiragen ruwa guda biyu a daya daga cikin sabbin hare-haren da ta kai a yankin.

0042 GMT — Asibitin da aka kai hari a Gaza ya daina aiki, an kwashe marasa lafiya — WHO

Wani asibiti a arewacin Gaza da sojojin Isra'ila suka kai samame ya daina aiki, kuma an kwashe marasa lafiya ciki har da jarirai, lamarin da ya ƙara jefa ayyukan kiwon lafiya da ke rugujewa a yankin cikin hadari, in ji wani jami'in Hukumar Lafiya ta Duniya.

Richard Peeperkorn, wakilin WHO a Gaza, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Abin da muka fahimta shi ne asibitin ya daina aiki kuma."

Ya ce an mayar da jarirai biyu da aka haifa gida zuwa ga iyalansu tare da bayanin yadda za su kula da su, yayin da aka kwashe sauran marasa lafiya ciki har da jarirai zuwa asibitocin Al Ahli da Al Shifa.

"An ce an tsare ma'aikatan lafiya da yawa," in ji shi. Ya kara da cewa "Ba za mu iya juriyar sake yin asarar kowane asibiti ba."

Yayin da aka tura da yawa zuwa kudancin Gaza, akwai rahotannin da ke cewa har yanzu mutum dubu dari na nan a arewacin kasar, inda "akwai bukatar samar da cibiyoyin kiwon lafiya da dama," in ji Peeperkorn.

Ya kuma ce kimanin mutum 4,000 da suka rasa matsugunansu da suka fake a harabar asibitin Nasser da ke kudancin birnin Khan Younis na cikin hadari yayin da Isra'ila ta kai hari a yankin. "Sun gaya wa ma'aikatanmu cewa suna jin tsoro sosai," in ji Peeperkorn.

#