Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 218, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,943 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,572 ne suka jikkata.

KAI-TSAYE: Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyaka

0947 GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyaka

Kungiyar Hezbollah a ranar Asabar ta ce ta kai hari kan wani gini wanda sojojin Isra'ila suka taru a kusa da iyakar Lebanon da ke kudancin ƙasar.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce mayaƙanta sun kai hari kai tsaye kan "wani gini wanda sojoji suke a Metula da makamai masu kyai.

Harin ya kasance "a matsayin martani ga hare-haren da masu tsatsauran ra'ayin Yahudawa suka kai kan ƙauyukan kudanci da gidajen fararen hula, wanda na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai a garin Tayr Harfa," in ji Hezbollah, yayin da ƙungiyar ke magana kan harin na ranar Juma'a wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu.

#