Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Alhamis, 1 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.

KAI TSAYE: Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansanin gudun hijira na Bureij a Gaza

1401 GMT — Gomman mutane sun mutu a harin Isra'ila kan wata makaranta da sansanin gudun hijira na Bureij a Gaza

Ƙungiyoyin agaji da ke aiki a yankin Gaza da ke cikin ƙawanya sun ce aƙalla gawar mutum 15 aka gano a ƙarƙashin baraguzai bayan da Isra'ila ta kai wani harin sama a kan sansanin ƴan gudun hijira na Bureij.

Kazalika wasu mutum 27 din sun mutu a wani harin daban da aka kai kan wata makaranta mallakar Majalisar Dinkin Duniya, a cewar Ma'aikatar Lafiya da Gazan.

1244 GMT — Isra'ila ta kai hare-haren sama fiye da sau 12,000 cikin Gaza tun 7 ga Oktoba

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ƙasar ta kai hare-haren sama fiye da sau 12,000 cikin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba.

Wata sanarwa ta ce an kai harin kan dubban wurare a yayin wadannan hare-hare.

A wannan makon, rundunar sojin Isra'ila ta faɗaɗa kai hare-harenta ta sama da ta ƙasa cikin Gaza, wacce ke cikin uƙubar hare-haren Isra'ilan tun bayan wani harin ba-zata da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

#