Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 56 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 16,000, galibinsu mata da kananan yara. Kimanin mutum 7,000 aka danne a baraguzan gine-gine wadanda Isra'ila ta yi wa luguden wuta, a cewar hukumomi.

KAI-TSAYE: An kashe sama da Falasdinawa 60 a hare-haren Isra'ila a Gaza

1156 GMT — An kashe sama da Falasdinawa 60 a hare-haren Isra'ila a Gaza

Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce sama da mutane 60 ne suka mutu sakamakon ci gaba da gwabzawa tsakanin Isra'ila da Hamas bayan ƙarewar wa'adin tsagaita wuta.

A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce ta kuma tattara "sauran mutane da dama a suka jikkata a harin da aka kai ta sama kan fararen hula".

1003 GMT — Isra'ila ta wallafa taswirar da ta raba Gaza zuwa 'tudun-mun-tsira

Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wata taswira da ta karkasa yankin Gaza zuwa daruruwan rukunai sannan ta umarci mazauna yankin su yi nazarinsa domin ganin inda za su iya guduwa domin tsira.

An gididdiba Gaza zuwa layi da tituna a wasu bangarori na taswirar. An wallafa taswirar awanni bayan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda da Qatar, Masar da Amurka suka shiga tsakani ya zo karshe.

Kafin tsagaita wutar, yakin ya fi zafi ne a arewacin Gaza, inda Isra'ila ta aike da dakaru ta kasa. sai dai yanzu, da alama yakin ya mayar da hankali kudancin Gaza, inda Falasdinawa kusan miliyan 2 suke zaune, ciki har da wadanda suke tsere daga arewaci.

0659 GMT — Ana 'ci gaba' da tattaunawa duk da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza

Qatar da Masar suna ci gaba da shiga tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa duk da sabbin hare-haren da dakarun Isra'ila suka kaddamar da safiyar Juma'a a Gaza, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa game da ci gabada kai hare-hare da Isra'ila ke yi a Gaza, tana mai cewag "wadanda ke kan mulki sun yanke shawarar ci gaba da kashe kananan yara." / Hoto: AA

"Qatar da Masar na ci gaba da shiga tsakani domin yin sulhu duk da cewa Isra'ila ta sake kaddamar da hare-hare a Gaza," a cewar majiyar wadda ba ta so a ambaci sunata saboda sarkakiyar lamarin, bayan an jwashe dare ana tattaunawa wadda ta gaza cim ma matsaya don tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta zuwa kwana na takwas.

A gefe guda, wata sanarwa da Ma'aikatar Wajen Qatar ta fitar ta bayyana matukar takaici kan hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kaiwa a Gaza, tana mai cewa "sabbin hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza suna dagula yunkurin shiga tsakani."

Dakarun Isra'ila sun kai jerin hare-hare a gidajen kwanan jama'a a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. 

0607 GMT — Isra'ila ta kashe mutane da dama bayan wa'adin yarjejeniyarta da Hamas ya kare

Falasdinawa akalla shida ne suka mutu yayin harin da Isra'ila ta kai ta sama a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Falasdinu Ashraf al Qudra ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

A gefe guda, an kashe kananan yara biyu a hari ta sama da Isra'ila ta kai a Birnin Gaza, a cewar Fadel Naim, wani likita a asbitin Al Ahli, a yayin da aka ci gaba da gumurzu tsakanin Hamas da Isra'ila bayan karewar wa'adin tsagaita wuta.

Dakarun Isra'ila sun kai jerin hare-hare a gidajen kwanan jama'a a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Wasu majiyoyi sun ce an garzaya da gawawwaki hudu da kuma wasu mutane asibitin Abu Youssef Al Najjar da ke birnin Rafah bayan dakarun Isra'ila sun kai musu hari.

Kazalika Isra'ila ta kai hari a wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Al Maghazi da ke tsakiyar inda ta kashe wani Bafalasdine tare da jikkata mutum hudu. Jami'an kiwon lafiya sun tabbatar wa kamfanin dillancin labara na Anadolu wadannan hare-hare.

Isra'ila ta sanar da ci gaba da kai hare-hare Gaza bayan karewar wa'adin yarjejeniyarta da Hamas. / Hoto: Reuters

0500 GMT — Isra'ila da Hamas sun ci gaba da gumurzu a Gaza

Rundunar Sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta ci gaba da kai hare-hare a arewacin Gaza da jiragen yaki da tankoki da kuma jiragen ruwan soji.

Ta bayyana haka ne ranar Juma'a bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ya kare.

Bayanai sun ce yaki ya kaure tsakanin sojojin Isra'la da Falasdinawa masu fafutuka a arewaci da tsakiyar Gaza bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ya kare

Wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas ya kare ne ranar Juma'a da safe./Hoto: AFP

0250 GMT — Isra'ila da Hamas sun amince da tsawaita tsagaita wuta zuwa rana ta takwas - WSJ

Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas sun amince da tsawaita tsagaita wuta zuwa kwana na takwas, a wata yarjejeniya da za ta ƙunshi sakin wasu ƙarin fursunonin Falasdinu da suke tsare a gidan yarin Isra’ilan, da kuma Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su, kamar yadda gidan jaridar Wall Street Journal ya ambato jami'an Masar suna faɗa.

0250 GMT — Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce motocin agaji 65 ne suka shiga birnin Gaza na arewaci

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bayyana cewa, jimillar manyan motocin agaji 65 ne suka shiga birnin Gaza da kuma arewacin Gaza.

Wannan ya kawo adadin manyan motocin da aka aika zuwa 310 tun bayan da aka dakatar da ayyukan jinƙai a ranar 24 ga Nuwamba.

Sanarwar ba ta yi nuni da ko an aike da motocin man fetur zuwa yankunan biyu ba.

Motoci bakwai dauke da mai da iskar gas sun shiga yankin Zirin Gaza ta kan iyakar Rafah, kamar yadda Wael Abu Mohsen, shugaban sadarwa na bangaren Falasdinawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya yi kira tun da farko da a kara tsawaita zaman sulhun. / Photo: AA

0230 GMT Isra'ila ta kama Falasdinawa 3,390 a Yammacin Kogin Jordan tun ranar 7 ga Oktoba

Sojojin Isra'ila sun tsare Falasdinawa 3,390 a hare-haren da suka kai a yankin Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye tun ranar 7 ga watan Oktoba, ciki har da 260 din da aka kama a lokacin da aka tsagaita wuta, in ji kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar fursunoni ta Falasdinu da hukumar kula da fursunonin suka fitar, ta ce an kama mutanen ne a cikin gida da kuma wuraren binciken sojoji da suka hada da wadanda aka tilasta musu miƙa wuya sakamakon matsin lamba da kuma wadanda aka yi garkuwa da su.

A ranar Alhamis ne aka kama mutum 30, yayin da adadin wadanda aka kama a ranar Laraba zuwa daren Alhamis ya kai 40, in ji su.

0146 GMT — Wani ɗan Isra'ila da ke tsare a hannun Hamas ya roƙi Netanyahu ya kwaso gawarwakin iyalinsa daga Gaza

Wani ɗan Isra'ilan da ke tsare a hannun ƙungiyar Hamas ya roƙi Firaminista Benjamin Netanyahu ya tsara yadda za a kwaso gawarwakin iyalinsa daga Gaza tare da yi musu jana'iza a Isra'ila, bayan da suka mutu a wani harin sama na Isra'ilan da ta kai yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya a lokacin da suke tsare a wajen Hamas.

Roƙon ya zo ne a cikin wani saƙon bidiyo da rundunar Qassam ta Hamas masu dauke da makamai, ta fitar.

“Bibi [Netanyahu], kun jefa bam tare da kashe matata da ’ya’yana biyu, wadanda su ne abu mafi muhimmanci a rayuwata,” in ji Yardin Bibas.

"Ina roƙonka ka mayar da iyalina zuwa ƙasarsu domin a binne su a Isra'ila, "in ji shi cikin yanayi na tausayi.

“Bibi, ina roƙonka ka mayar da su Isra’ila, don Allah ka dawo da su gida.

#