Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 302, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 39,500 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 91,000, kana mutum fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine.

Kai-tsaye: Amurka ta tura jiragen ruwan yaƙi da manyan jirage da na'urorin kakkaɓo makamai Gabas ta Tsakiya

Asabar, 3 ga watan Agusta, 2024

2142 GMT — Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya bayar da umarni a tura jiragen ruwa na yaƙi da manyan jirage yankin Gabas ta Tsakiya bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi a Iran da Lebanon, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon.

Kazalika Amurka ta aika da ƙarin tawaga ta jiragen sama na yaƙi da na'urorin kakkaɓo makamai masu linzami, in ji Pentagon.

Amurka na ɗaukar waɗannan matakai ne domin tunkarar barazanar da Iran da ƙawayenta suka yi kan yin martani bayan kisan gillar da Isra'ila ta yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyeh kwana biyu da suka wuce a Tehran da kuma kisan da ta yi wa babban kwamandan Hezbollah a Beirut a yayin da take ci gaba da aiwatar da kisan ƙare-dangi a Gaza.

"(Austin) ya shaida wa ministan tsaron Isra'ila ƙarin matakan da ma'aikatar tsaro take ɗauka da suka haɗa da sauye-sauyen da za su tabbatar da tsaron Isra'ila," in ji kakakin Pentagon Sabrina Singh a yayin da take bayar da sanarwa ga manema labarai.

"Ta ƙara da cewa, "(Austin) ya tabbatar wa minista Gallant da Shugaba Joe Biden da kuma Firaminista Benjamin Netanyahu cewa za mu tura ƙarin matakan tsaro domin kare yankin."

#