Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 144 - ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 29,782, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 69,879.

KAI-TSAYE: Amurka ta ce akwai yiwuwar Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare Gaza a lokacin azumin Ramadana

0831 GMT — Amurka ta ce akwai yiwuwar Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare Gaza a lokacin azumin Ramadana

Shugaba Joe Biden ya ce Isra'ila za ta amince ta dakatar da yakin da take yi a zirin Gaza a lokacin azumin watan Ramadana mai zuwa idan har aka cimma matsaya na sako wasu daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

Masu shiga tsakani daga kasashen Amurka da Masar da kuma Qatar na aiki kan wani shiri na yarjejeniya wadda a ƙarƙashinta ake sa Hamas za ta saki fursunonin yaƙi da dama da ta yi garkuwa da su, inda ita kuma Isra’ila ta sako fursunonin Falasɗinawa da kuma tsagaita wuta tsawon makonni shida.

A lokacin tsagaita wutar ta wucin-gadi, za a ci gaba da tattaunawa kan sakin sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

0212 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ta'azzara

Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu na WAFA ya rawaito cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa uku a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye.

An kashe mutanen ne a harin da aka kai a garin Tubas da kuma sansanin Al-Far’a da ke kusa da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, in ji sanarwar.

Aƙalla Falasɗinawa 400 ne sojojin Isra'ila da wasu Yahudawa ƴan kaka-gida suka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba.

2300 GMT — Biden ya ce ana dab da tsagaita wuta a Gaza yayin da Isra'ila ke shirin mamaye Rafah

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana fatan tsagaita wuta a Gaza da aka yi wa ƙawanya ka iya fara aiki a farkon mako mai zuwa.

Da ya ziyarci birnin New York, an tambayi Biden lokacin da tsagaita wuta a yankin Falasdinawa da aka killace zai iya farawa, ya kuma amsa da cewa, "Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa ya gaya mini cewa muna kusa, mun kusa, ba mu gama ba tukuna. Fatana shi ne nan da Litinin mai zuwa za a tsagaita wuta."

#