Zanen muhalli a Afirka yana haɓaka a wani salon fasahar ƙirƙira da ke nuna al'adu, tare da shawo kan matsaloli kamar buƙatun al'umma da sauyin yanayi.

Jovanie: Yadda masanin zanen muhalli yake haɗa salon Afirka da na zamani

Daga Firmain Eric Mbadinga

Yana da ban mamaki a ce an yi amfani da kayan aikin mai zanen muhalli na yau da kullum, wato takarda, fensiri, da rula, domin a sauya tarihi.

Daga tsaffin ƙasashe kamar Girka, zuwa Afirka a yau, fagen zanen muhalli yana nuna bajintar al'adu da al'umma, tare da sauyin tunani da buri.

Alal misali a Masar, an gina gidajen tarihi masu siffar dala waɗanda aka gina a shekarun 2,550 da 2,490 BC, suna nuna salon zanen muhalli, wanda fage ne da ke nuna bambancin tushensu.

Idan masu hikimar zamanin Renaissance kamar su Michelangelo da Leonardo da Vinci sun ƙirƙiri jadawalin zane na zamani, masu zane a Afirka yanzu suna bayyana salonsu ta amfani da bulo da siminti.

Masanin zanen muhalli ɗan Gabon, Jovanie Sonie Ndong Songo, wanda ya samu horo a jami'ar ƙasashen Yamma, yana nuna salon al'umma mai ilimi kan salon zane na dauri, amma kuma mai tasowa daidai da buƙatun yau da na gobe.

Ya yi imani cewa zanen muhalli ya shafi yanayin gari da manufar bayyana tunani da salon fasaha.

Jovanie ya faɗa wa TRT Afrika cewa, "Francis Kéré da Christian Benimana mutane ne da ke aiki don ɗaukaka fagen zane mai la'akari da al'adun gargajiya, daidai da muƙatun al'ummar nahiyar".

Tarin albarkatu

Domin tafiya da zamani, an fito da sabbin manhajojin kwamfuta cikin kayan ayyukan zane. Akwai shirye-shirye da salo-salo da aka gabatar a taswirar 3D kuma da taimakon ƙirƙirarriyar basira.

Salon zanen muhalli a Afirka zai iya samar da fitaccen salon al'adu. / Hoto: Jovanie Sonie Ndong Songo

Zaɓin kayan yin gini shi ne babban ƙalubale wajen gini da zai nuna salon zane kuma ya bayyana darajar aikin. Ko dai katako, ko ƙarfe, dutse ko siminti, inganci da yawan kowane sinadari yana da muhimmanci a tunanin mai zane.

A Afirka, sanannen kwatancen zanen muhalli yana bayyana a yawan amfani da kayayyakin gargajiya kamar itace, da kaba, da ƙasar terracotta.

Sanannun bine-gine kamar Babban Masallaci a Benin da kuma ginin Mapungubwe Interpretation Centre a Afirka ta Kudu suna bayyana arziƙi da yalwar zanen muhalli a Afirka.

Jovanie ya ce, "Duk da ƙalubale da tasirin baƙi, zane muhalli a Afirka yana ci gaba da haɓaka, da dacewa da fitowa fili a matsayyin keɓantaccen salon ƙirƙira a nahiyar".

A yawancin tarukan ƙasa-da-ƙasa kan zanen muhalli, ana tattaunawa kan matsalolin zamani wajen rungumar sabbin fasahohi, da alkinta sarari, da kiyaye sauyin yanayi.

Ɗaukaka buƙatun al'umma

Masu zane a Afirka suna fuskantar matsaloli kamar na tsara gine-gine da ba su da tsada, kuma suke da siffofin salon ginin gargajiya da suka dace da yanayin yankuna dabn dabna na nahiyar.

Jonanie ya ƙara da cewa, "Ƙara wayar da kai, da horo da haɓaka salon zane mai ɗorewa yana da muhimmanci idan har muna son cimma ƙalubalenm da ke fuskantar harkar gini a Afirka".

Masu zane suna da aniyar haɗa al'adar Bantu, da zmani, da girmama muhalli. / Hoto: Jovanie Sonie Ndong Songo

A ƙasarsa ta haihuwa, Gabon, fagen zanen muhalli harka ce ta gina birane. Masu zane suna da aniyar haɗa al'adar Bantu, da zamani a ayyukansu. Sauyin yanayi, wadda matsala ce da ta shafi dukkan duniya, wani batu ne da ake dubawa.

Jovanie ya bayyana cewa, "kare muhallin da muke da su kamar fadamu, da dazuka, da gandu, yana da muhimmanci don kaucewa mayar da yankuna noma zuwa birni. Wannan zai taimaka wajen kiyaye yanayin mai juriya sanda ake tsaka da sauyin yanayi".

Ayyuka don kawar da sauyin yanayi sun haɗa da kulawa da nau'in dabbobi da tsirrai, da kula da ƙasa da muhalli, da cigaba mai ɗorewa.

Kula da yanayin yayin tsara birane ta hanyar gina gandun daji da wuraren shukoki shi ma wani muradi na zanen muhalli. Kenan kare fadamu da maido da hanyoyin ruwa na asali zai rage haɗarin ambaliya da kare muhalli.

Waɗanda ke zamani da Jovanie kamar Kéré daga Burkina Faso da Benimana daga Tanzania, sun karɓi ra'ayin ba da muhimmanci kan zana gini da zai dace da yanayi da al'adun nahiyarmu.

Ba a Afirka ba kawai

A Maris na 2022, Kéré ya zama ɗan Afirka na farko da ya ci kyautar zanen muhalli ta Pritzker Architecture Prize, wadda ke yabawa kan "aikin mai zanen da ke raye wanda ya nuna, ta hanyar ayyukan da ya yi, mabambantan ɓangarorin hazaƙarsa kuma ya yi tasiri babba ga harkar zanen muhalli".

Jovanie yana da ayyukan da yake burin nuna bajintarsa a fannin gine-gine na ƙasarsa da fannin tsara birane da ma wasu fannonin.

Wadannan ayyuka suna zuwa tare da ƙarin nauyin cewa "a Afirka aka yi su", wanda ke da muradin fitar da dabaru da salon zane a Afirka da kuma ƙwararrun zuwa sassan duniya.

Jovanie ya ba da shawarar dabaru masu yawa don tabbatar da zanen Afirka ya samu farin jin a duniya. Wannan ya haɗa da ɗaukaka fasaha, gina dabaru daidai da yankin kasuwanci, da ɗaga darajar fagen al'adu.

Mai zanen wanda ɗan Gabon ne ya kuma shawarci a ƙarfafa batun haƙƙin mallakar fasaha.

Ayyukan Kéré sun yi suna wajen tasiri kan al'umma da haɗa buƙatun alkinta al'adu da nda gargajiya, daidai da yadda suke haɗowa da buƙatar cigaa mai ɗorewa a duka harkar gini a faɗin Afirka.

Ana yaba wa Benimana, wanda ya yi aiki kan ayyuka da dama a Afirka, kan aksancewarsa gwani wajen hangen nesa a fannin da ya ƙware.

Da yake fayyace bayani kan babban jigon da ya fi fice a aikinsa, ya ce, ''Na yi imani cewa zane muhalli ba kawai zana gini ba ne, amma ya ƙunshi ɗaukaka mutunci yadda zai yi tasiri mai ɗorewa".

Duka waɗannan masu aikin sun haɗu wajen kira da a yi duba na musamman kan masu fikira da ƙwararru 'yan Afirka idan ana batun kiran kwararrun da za su yi kwangilar gina sabbin gine-gine.

#