Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban Turkiyya Erdogan ya bayyana damuwarsa, yana mai cewa ana ci gaba da ayyukan ceto tare da hadin kai da jami'an yankin.

Jirgin dakon kaya na sojin Turkiyya ya yi hatsari a iyakar Georgia-Azerbaijan dauke da jami'ai 20

Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta bayyana ranar Talata cewa sojoji 20 na Turkiyya suna cikin jirgin soja mai ɗaukar kaya na C-130 wanda ya yi hatsari a kusa da iyakar Georgia da Azerbaijan yayin da yake kan hanyarsa daga Azerbaijan zuwa Turkiyya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar tun da fari, ma'aikatar ta ce jirgin "ya tashi daga Azerbaijan zuwa ƙasarmu kuma ya yi haɗari a kan iyakar Georgia da Azerbaijan," ta ƙara da cewa ana ci gaba da ayyukan bincike da ceto "a karkashin haɗin gwiwa da hukumomin Azerbaijan da Georgia."

Babu wani bayani da aka fitar har yanzu game da ko akwai wadanda suka tsira ko samun asarar rai.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce ya labarin hatsarin "abin matuƙar baƙin ciki ne," yana tabbatar da cewa ana ƙoƙarin isa inda tarkacen jirgin yake.

A wani rubutu a shafin X, Erdogan ya ce: "Ana ci gaba da kokari na haɗin gwiwa da hukumomin da abin ya shafa don isa inda tarkacen jirgin yake. Allah ya jiƙan shahidanmu."

Ma'aikatar ta ce an kaddamar da bincike don gano musabbabin hatsarin.

Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ma ya kira Erdogan ya miƙa masa ta'aziyya kan hatsarin jirgin.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#