Dollar

42,5985

0.02 %

Euro

49,6462

0.08 %

Gram Gold

5.716,1800

-0.36 %

Quarter Gold

9.509,9300

0 %

Silver

79,2200

-0.44 %

Iran ta ce jirgi ɗauke da kashi na biyu na waɗanda aka tasa ƙeyarsu zuwa gida ya tashi ne yayin da Washington ke ƙoƙarin mayar da ɗaruruwan mutane Iran.

Jirgin Amurka ya mayar da 'yan Iran 55 zuwa Tehran

Jirgi na biyu da ke ɗauke da Iraniyawa da aka tasa ƙeyarsu daga Amurka ya bar Amurka, kamar yadda jami’an Iran suka bayyana, yayin da Washington ke shirin mayar da ɗaruruwan ‘yan gidan yari zuwa Jamhuriyar ta Musulunci.

Tasa ƙeyar ‘yan ƙasar na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce tsakanin Iran da Amurka bayan Amurka ta kai harin bam kan tashoshin nukiliyar Iran a lokacin yaƙin kwanaki 12 da Tehran ta gwabza da Isra’ila a watan Yuni.

Wani rahoto da aka wallafa ranar Litinin a kafar watsa labaran Mizan, kafar sadarwar fannin shari’ar Iran, ya ambato jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran Mojtaba Shasti Karimi inda ya tabbatar da tasa ƙeyar ‘yan Iran 55 gida.

“Waɗannan mutanen sun bayyana amincewarsu da komawa gida sakamakon ci gaba da manufa ta ƙin shiga ƙasa da kuma manufa ta wariya ga baƙi, musamman ‘yan Iran da Amurka ke yi,” in ji Karimi .

Mai magana da yawun m’aikatar harkokin wajen Itan Esmail Baghaei ya kuma bayyana ranar Lahadi cewa ana shirin mayar da ‘yan Iran 55 Tehran.

Bisa ga iƙirarin Amurka, “an mayar da ‘yan Iran ne saboda dalilai na shari’a da kuma ƙeta dokokin shige da fice," a cewar Baghaei.

Gwamnatin Amurka ba ta amsa nan-take ba cewa jirgin mayar da ‘yan ƙasar ya tashi kuma babu tabbacin ko jirgin ya isa Tehran kawo yanzu.

Ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka da kuma ma’aikatar harkokin wajen Amurka ba su mayar da martani nan-take ba game da buƙatar tsokacin da kamfanin dillancin labaran The Associated Press ya yi ba ranar Litinin.

A cikin watan Satumba, jami’an Iran sun ce za a iya mayar da kimanin ‘yan Iran 400 a ƙarƙashi manufar gwamnatin Trump. A wancan watan ne irin wannan jirgin na farko ya sauka a Tehran.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#