Hukumomin Amurka sun soma bincike kan takardun zama ‘yar ƙasa na Omar da kuma bayanan shige da fice na mahaifinta da ya rasu yayin da 'yar majalisa ta zargi Trump da yi mata barazana ta siyasa.

Gwamnatin Trump na binciken Ilhan Omar, za ta ƙwace takardarta ta ‘yar ƙasa tare da korar ta: rahoto

Gwamnatin Trump ta ƙaddamar da wani bincike mai faɗi na tarayya kan 'yar majalisar dokoki ta Jam’iyyar Democrat Ilhan Omar da nufin kafa hujjojin shari'a da za su kai a ƙwace mata takardar zama ‘yar ƙasar Amurka da kuma korar ta daga ƙasar, in ji jaridar The Wall Street Journal.

Jaridar ta bayyana haka ne tare da ambato wasu jami'an Amurka da majiyoyi da suke da masaniya kan lamarin.


Binciken da ake yi mai sassa da yawa yana duba yadda Ilham Omar ta samu takardar zama ‘yar ƙasar Amurka bayan shigowar ta daga Somaliya a matsayin 'yar gudun hijira.

Haka kuma ya mayar da hankali kan takardunta da ayyukan mahaifinta, Nur Omar Mohamed, wanda ya kai iyalansa Amurka daga sansanin 'yan gudun hijira na Kenya a shekarar 1995.


Abin da binciken ya fi mayar da hankali a kai shi ne ko an canza shekarunta a kan takardunta na zama ‘yar ƙasa don nuna cewa tana da shekaru 17 maimakon 18, wanda ya ba ta damar samun shaidar zama ‘yar ƙasa kai-tsaye ta hanyar mahaifinta a shekarar 2000.


Binciken Tsaron Cikin Gida ya sake duba irin waɗannan zarge-zargen a ƙarƙashin gwamnatin Biden amma ya soke su saboda rashin samun shaidar aikata ba daidai ba.


Binciken ya tsananta sosai a ranar Litinin lokacin da jami'an gwamnatin tarayya suka gudanar da samame a gidan Ilham Omar da ke Washington, DC, makonni uku kacal kafin zaɓen tsakiyar wa'adi inda take neman sake tsayawa takara.


Masu bincike sun ƙwace wayarta ta hannu da kwamfutocinta da littattafan rubutu da kuma fasfo ɗinta.


Kazalika hukumomi sun bayar da gommam sammacin neman a ba su shaida a gaban babbar kotun tarayya a Minnesota, ciki har daga iyalan Omar.


Ƙoƙarin take  'yanci da barazanar siyasa
Omar ta yi Allah wadai da binciken, tana mai kiran matakin a matsayin "yunƙurin kama-karya" don tsoratar da abokan hamayya.


"Kada ku yi kuskure: wannan yunƙuri ne na kai hari ga maƙiyan siyasa da kuma amfani da makamai ga dokokin Ƙasa," kamar yadda Omar ta rubuta a shafinta na X, tana mai ƙari da cewa: "Ba za a rufe min baki ba."


Shari'ar wani ɓangare ne na binciken da gwamnati ke yi kan cancantar matsayin 'yan ƙasa da aka amince da su, tare da shigar da ƙararraki fiye da 200 zuwa yanzu.


Idan har za a kwace 'yancin zama ɗan kasa na mutum, to dole sai ma'aikatar Shari'a ta shigar da ƙarar tarayya da ke tabbatar da cewa an aikata zamba.


A wani ɓangaren kuma, Jeanine Pirro, Babbar Lauyar Amurka a Washington, ta tabbatar da cewa ofishinta na gudanar da bincike kan bayanan harkokin kuɗi da Omar ta bayyana.

#