Ƙungiyar ECOWAS ta janye duka takunkuman kasuwanci da ta saka kan Jamhuriyar Nijar. Haka kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa kasar Guinea.
Ƙungiyar ECOWAS ta sanar da cewa za ta cire takunkumin da ta saka a kan Nijar wanda ya haɗa da batun rufe iyaka da kuma kasuwanci.
Ta bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin taron da ta gudanar. Haka kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa kasar Guinea.
Tun a farkon watan nan ne Mali da Burkina Faso da Nijar suka sanar da ƙungiyar kan niyyarsu ta barin ƙungiyar, wanda wannan sabon lamari ne tun bayan kafa ƙungiyar a 1975.
Sai dai tun a jawabinsa na farkom Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa:
"Dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu,” in ji Tinubu.
“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.