Turkiyya ta jaddada muhimmancin yarjejeniyar tsagaita wuta, domin kawo karshen arangama da kuma cikas wurin kai kayayyakin agaji Gaza, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Duniya ta zura wa Isra'ila ido tana aikata laifukan yaki: Shugaba Erdogan

Isra’ila na aikata laifukan yaki a idon duniya ta hanyar kai hare-hare asibitoci da makarantu da wuraren ibada da masallatai da coci-coi har da kan motocin da ke dauke da marasa lafiya da matattu da sansanonin ‘yan gudun hijira, kamar yadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana.

Erdogan ya amsa tambayoyin ‘yan jarida kan dawowar da ya yi da jirgi daga Saudiyya a ranar Asabar, inda ya halarci taron Musulunci na musamman karo na takwas inda ya hadu da takwarorinsa domin tattaunawa kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza da kuma kokarin da ake yi domin kai wa fafaren hula agaji da kuma matakan samun mafita.

“Falasdinu wadda ke fama da mamaya da zalunci tsawon gomman shekaru, na fuskantar abubuwan da baki ba zai iya fada ba har tsawon kwanaki 36. Farar hula da ba su ji ba su gani ba na rasa rayukansu sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kaiwa ta sama inda ake raba su da muhallansu karfi da yaji,” in ji Erdogan.

Yayin da yake tabbatar da cewa kasashen yammacin duniya suna kallon duk wadannan munanan laifuka ne kawai daga ofisoshinsu, Erdogan ya ce wadanda ke da hankali ba za su iya yin shiru ba a irin wannan hali.

“Tun daga 7 ga watan Oktoba, mun ta yin iyakar kokarinmu domin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar diflomasiyya da tattaunawa”.

#