Dollar

41,1470

0.24 %

Euro

48,1391

0.07 %

Gram Gold

4.562,3600

1.18 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana yadda ma'aikata da dama na kamfanin dillancin labarai na Reuters suka fallasa yadda editoci da shugabannin kamfanin ke nuna goyon baya ga Isra'ila a yaƙin da take yi da Gaza.

Daga Ma'aikatan Reuters: 'Labaranmu suna lulluɓe irin walahar da Falasɗinawa suke sha'

Wasu ma'aikatan kamfanin dillancin labarai na Reuters da ke ƙasar Birtaniya, sun yi bayani a cikin wani rahoto da aka fitar a ranar Alhamis game da abin da suka kira son kai da nuna goyon baya ga Isra'ila daga ɓangaren editoci da shugabannin kamfanin.

A farkon wannan watan, bayan Isra'ila ta kashe ɗan jaridar Falasdinawa Anas Al Sharif, Reuters ta wallafa wani labari mai taken, "Isra'ila ta kashe dan jaridar Al Jazeera da ta ce shi jagoran Hamas ne." Wannan zabi na taken ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman ganin cewa Al Sharif ya taɓa kasancewa cikin tawagar Reuters da ta lashe lambar yabo ta Pulitzer a shekarar 2024, kamar yadda Declassified UK ta ruwaito.

Taken labarin ya haifar da martani mai zafi a shafukan intanet tare ƙara samun da damuwa a tsakanin ma'aikatan Reuters, inda wasu daga cikinsu suka bayyana damuwarsu a sirrance game da abin da suka kira nuna goyon baya a ra’ayin editocin kamfanin.

Reuters, wanda aka kafa a birnin London a shekarar 1851 kuma yanzu yana isa ga mutum fiye da biliyan ɗaya a kullum, yana fuskantar ƙarin bincike daga cikin gida.

Wasu ma'aikatan yanzu da na baya na Reuters, waɗanda suka yi magana a sirrance da Declassified UK, sun bayyana al'adar wata al’ada da editocin kamfanin suke da ita na rashin bayar da muhimmanci ga labarin Falasɗinawa.

Wani edita ya yi murabus a watan Agustan 2024, ya ce ya yi murabus ɗin ne sakamakon ɗabi’un kamfanin ba su dace da yadda suke bayar da rahoto a kan yaƙin da Isra’ila ke yi da Gaza ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#