Sport
Dollar
41,4171
0.21 %Euro
48,7056
-0.32 %Gram Gold
4.902,8900
1.34 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne ranar 18 ga watan Satumba bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa.
Sojojin Saman Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda fiye da 25 a wani samame da suka kai da cikin dare a yankin Bula na Jihar Yobe da Banki a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Mai magana da yawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame, shi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.
Ejodame ya ce jiragen yaƙinsu sun kai samamen ne ranar 18 ga watan Satumba bayan sun samu bayanan sirri daga sojojin ƙasa.
Ya ƙara da cewa masu tattara bayanan sirri sun bi diddigin yadda rukunonin ‘yan ta’adda suke kai komo sannan suka miƙa bayanan ga sojojin sama inda nan-take suka yi musu luguden wuta a arewacin Banki.
“Jiragen yaƙin sun kai samame uku a kan ‘yan ta’adda a yayin da suke kai komo da kuma lokacin da suka taru a maɓoyarsu, inda suka kashe mayaƙa fiye da 25,” in ji Air Commodore Ejodame.
Comments
No comments Yet
Comment