Wani wakilin fannin yawon buɗe ido ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Antalya ya karɓi masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje duk da ƙalubalen duniya

Birnin Antalya na Turkiyya ya karɓi kusan masu yawon buɗe ido miliyan 14 daga ƙasashen waje tun farkon shekarar 2026, lamarin da ke nuna yadda fannin yawon buɗe ido na birnin ke jure ƙalubalen duniya, ciki har da rikicin Gabas ta Tsakiya, yaƙin Rasha da Ukraine da matsalolin tattalin arzikin duniya.

Wani wakilin fannin yawon buɗe ido ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Kaan Kasif Kavaloglu, shugaban Ƙungiyar Masu Otel-otel ta Yankin Bahar Rum (AKTOB), ya ce kakar yawon buɗe ido ta bana ta samu nasara duk da raguwar masu yawon buɗe ido daga ƙasashen waje da kashi 5 cikin 100, sakamakon rikice-rikicen siyasa da tsaro a yankin da kuma durƙushewar tattalin arziki a wasu sassan Turai.

Kavaloglu ya ce fannin yawon buɗe ido na Antalya ya nuna juriya duk da yaƙin da aka shafe kusan shekaru biyar ana yi tsakanin Rasha da Ukraine, waɗanda ke daga cikin muhimman kasuwannin masu yawon buɗe ido na birnin.

Ya ƙara da cewa an samu gagarumin ƙaruwa a yawan baƙi daga Ukraine, Uzbekistan da Hungary a bana, lamarin da ya taimaka wajen rage tasirin raguwar baƙi daga wasu kasuwanni.

Ya ce hutun kaka na Herbstferien a Jamus ya riga ya fara, yayin da masu yawon buɗe ido daga Birtaniya da Rasha ke shirin yin hutu a wannan lokaci. A cewarsa, farashin yawon buɗe ido a watan Oktoba ya fi sauƙi idan aka kwatanta da Yuli da Agusta, lokacin da ake samun yawan masu yawon buɗe ido a lokacin zafi.

Kavaloglu ya kuma bayyana cewa Antalya za ta karɓi baƙuncin taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi, COP31, a watan Nuwamba, inda aka riga aka fara shirye-shiryen tarbar manyan baƙi.

#