Wani bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ɗauka ya nuna jama’a sun taru a wurin yayin da wata na’urar haƙa ƙasa ke kwashe baraguzan ginin.

Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya

Wani gini mai hawa 12 da ake kan ginawa ya rushe a ranar Jumma’a a birnin Nairobi, babban birnin Kenya, inda ofishin gwamnan jihar Nairobi ya ce ana fargabar wasu mutane sun makale a ƙarƙashin baraguzan ginin.

Har yanzu ba a gano musabbabin rushewar ginin ba.

Ofishin Gwamna Johnson Sakaja ya bayyana cewa ana amfani da benen ƙasa na ginin da ya rushe a unguwar Eastleigh.

Wani bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ɗauka ya nuna jama’a sun taru a wurin yayin da wata na’urar haƙa ƙasa ke kwashe baraguzan ginin.

Wasu bidiyoyi da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda ginin ya rushe kwatsam, inda ƙura mai yawa ta turnuƙe sararin samaniya a wannan yanki mai cunkoson jama’a, wanda ya ƙunshi wuraren kasuwanci da gidajen zama.

’Yan jaridar kamfanin dillancin labarai na AFP da suka je wurin sun ga yadda ginin ya koma tarkace, yayin da jami’an ceto suka isa domin fara aikin bincike da ceto mutanen da ka iya kasancewa a ƙarƙashinsa.

AFP ta kuma ruwaito cewa ’yansanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa jama’ar da suka taru kusa da wurin.

A halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da ayyukan gine-gine cikin sauri a Nairobi, inda ake ta gina manyan gine-gine masu hawa da dama a sassa daban-daban na birnin, musamman a Eastleigh, wadda ta shahara da manyan kasuwanni da cunkoson jama’a.

Sai dai ana ci gaba da nuna damuwa kan batun tsaron gine-ginen.

Bisa ga alkaluman hukumar ƙididdiga ta Kenya, yawan gine-ginen da ake kammalawa a Nairobi a kowace shekara ya ƙaru daga 20,025 a shekarar 2022 zuwa 25,090 a shekarar da ta gabata.

#