Baya ga haka ƙasar ta Amurka ta kori mutane daban-daban zuwa ƙasashensu, kuma ana sa ran ƙasar za ta tasa ƙeyar ‘yan Nijeriya 85 zuwa ƙasarsu nan gaba.

Amurka ta gargaɗi 'yan Nijeriya kan tsawaita wa'adin zamansu a ƙasar

Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce duk mutumin da ya zauna a Amurka fiye da wa’adin bizarsa zai iya rasa damar sake shiga ƙasar har abada.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar a shafinsa na X ranar Litinin, ta ce jami’an ofishin jakadancin suna da bayanai game da duk wanda ya taɓa wuce wa’adin da aka ba shi na zama cikin Amurka.

“Babu wani ‘kuskure na gaskiya’ – amfani da bizarka yadda ya kamata nauyi ne da ya rataya a wuyanka,” in ji sanarwar.

Tun bayan zaɓen Shugaban Amurka Donald Trump ne dai ƙasar ta Amurka ta fara tasa ƙeyar baƙin-haure zuwa ƙasashensu.

Cikin waɗanda ƙasar take kora har da ɗalibai da masu izinin zama a ƙasar da suka shiga zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa da Hamas kan yaƙin da Isra’ila ke ƙaddamarwa a Zirin Gaza.

Baya ga haka ƙasar ta Amurka ta kori mutane daban-daban zuwa ƙasashensu, kuma ana sa ran ƙasar za ta tasa ƙeyar ‘yan Nijeriya 85 zuwa ƙasarsu nan gaba.

#